Isa ga babban shafi

Barcelona ta sha kashi a hannun Antwerp 3 da 2

Kungiyar kwallon kafa ta Royal Antwerp ta kasar Belgium ta  bai wa  Barcelona mamaki a wasan zakarun nahiyar Turai da bangarorin biyu suka fafata  daren Laraba, inda ta saka kwallaye 2 a ragar Barcelona kusan karshen wasa.

'Yan wasan Barcelona da Royal Antwerp yayin wasan su a gasar zakarun Turai.19/09/23
'Yan wasan Barcelona da Royal Antwerp yayin wasan su a gasar zakarun Turai.19/09/23 AP - Joan Monfort
Talla

Matashin dan wasa, Arthur Vermeeren ne ya ci wa Antwerp kwallo a cikin dakikoki 90 da fara wasa, kafin Ferran Torres ya farke wa Barcelona daf da hutun rabin lokaci.

Antwerp ta sake saka kwallo ta hannun Vincent Janssen, amma  Marc Guiu, mai shekaru 17 ya rama wa Barcelona a minti na 91, lamarin da ya sa aka yi tunanin za su raba maki.

Amma Antwerp ba ta yi kasa a gwiwa ba, inda wani matashin dan wasanta, Ilenikhena ya ci mata kwallo, aka Karkare wasan 3 da 2.

Antwerp ta yi rashin nasara a dukkanin wasannin rukunin H da ta buga a gasar zakarun Turai ta farko da ta samu zuwa, inda yanzu aka yi waje da ita.

Sai dai zakarun na Belgium, wadanda suka lashe kofin league din kasar a karon farko tun bayan 1957 sun jajirce don ganin cewa babu wanda ya bar wannan rukuni na su ba tare da ko da maki guda ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.