Isa ga babban shafi

Abubuwa 11 da ya kamata ku sani game da Hazard da ya yi ritaya daga Tamola

Tsohon dan wasan Chelsea da Real Madrid, Eden Hazard, ya sanar da yin ritaya daga buga kwallo yana da shekara 32.

Dan wasan kasar Belgium Eden Hazard kenan
Dan wasan kasar Belgium Eden Hazard kenan © guardian
Talla

 

A wannan Talata ce, tsohon kyaftin din na Belgium ya sanar a da haka cikin wani sako da ya wallafa a shafinsa na Instagram, bayan ya shafe shekaru 16 yana buga kwallo.

“Bayan shafe shekaru 16 a fagen taka leda, da doka wasanni sama da 700, na yanke shawarar kawo karshen sana’ata a matsayin kwararren dan kwallon kafa. Na kai ga cimma burina, na yi wasa yadda ya kamata kuma na samu nishadi a filayen wasannin daban-daban a duniya.”

Ga wasu abubuwa 11 da ya kamata ku sani game da Hazard;

1. An haifi Eden Hazard a ranar 7 ga watan Janairun shekarar 1991, a La Louvière na kasar Belgium.

2. Mahaifiyarsa, Carine, da mahaifinsa, Thierry, 'yan wasan kwallon kafa ne. Mahaifinsa ya shafe mafi yawan aikinsa a wani klub dake rukuni na biyu a Louvière na kasar Belgium.

3. Hazard ya fara wasan kwallon kafa tun yana dan shekara hudu a lokacin da ya koma kungiyarsa ta Royal Stade Brainois. Ya shafe shekaru takwas a kulob din kafin ya koma AFC Tubize. Ya koma Lille a shekarar 2005.

4. Hazard ya koma Chelsea daga Lille a ranar 1 ga watan Yulin shekarar 2012, kuma ya shafe shekaru 7 a kungiyar. Ya koma Real Madrid ne a ranar 1 ga watan Yulin 2019. A shekarar 2015 ya zama kyaftin din Belgium a kuma ya yi ritaya daga tawagar kasar a 2022.

Tsohon dan wasan Real Madrid Eden Hazard
Tsohon dan wasan Real Madrid Eden Hazard AFP/File

5. Hazard ya dokawa kasarsa ta Belgium wasanni 123 inda ya zura kwallaye 33 sannan ya taimaka aka ci 36.

6. A Chelsea kuwa ya buga wasanni 352 inda ya zura kwallaye 110 sannan ya taimaka aka zura kwallaye 92.

7. A Lille, Hazard ya buga wasanni 194, ya zura kwallaye 50 sannan ya taimaka 53.

Tsohon dan wasan Real Madrid Eden Hazard
Tsohon dan wasan Real Madrid Eden Hazard AFP

8. A Real Madrid Hazard ya buga wasanni 72 inda ya zura kwallaye 7 sannan ya taimaka aka ci 11.

9. Hazard ya lashe kyautar Gwarzon Dan Wasan Kwallon Kafar Ingila a shekarar 2015.

10. A Chelsea ya karbi kyautar gwarzon 3x na shekara sau daya, a Lille kuma sau biyu.

11. Hazard ya lashe gasar zakarun Turai na kakar 21/22 tare da Real Madrid, yana kuma rike da kofin FIFA Club World Cup na 2023 tare da Real Madrid. Hakanan kuma yana da kofunan Europa League guda 2 a kakar 2013 da 2019 tare da Chelsea.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.