Isa ga babban shafi

Eden Hazard ya sanar ritaya da ya fagen tamaula

Tsohon tauraron Chelsea da ya koma taka leda da Real Madrid ta Spain, Eden Hazard ya sanar da ritaya daga fagen tamaula a yau Talata, matakin da ke kawo karshen shekaru 16 da ya shafe yana take leda.

Dan wasan Real Madrid Eden Hazard yayin gogayya da 'yan kungiyar Cadiz a gasar LaLiga.
Dan wasan Real Madrid Eden Hazard yayin gogayya da 'yan kungiyar Cadiz a gasar LaLiga. AP - Jose Breton
Talla

Hazard dan Belgium mai shekaru 32 wanda ya koma Real Madrid daga Chelsea a shekarar 2019 kan farashin fam miliyan 89, amma kuma ya iya doka wasanni 54 kacal gabanin rabuwa da kungiyar a karshen kakar da ta gabata.

Hazard wanda ya lashe kofunan Firimiya 2 yayin taka ledarsa da Chelsea anga haskawarsa a wasanni fiye da 700 a tsawon lokacin da ya shafe yana taka leda a dukkan matakai.

Zakaran na Belgium wanda ya ke ba tare da kungiya ba, tun vayan da Real Madrid ta kawo karshen kwantiraginsa a watan Yuni, ya ce ya dauki matakin ne bayan sauraron zuciyarsa.

Eden Hazard wanda tun farko ya yi ritaya daga dokawa kasar shi leda, bayan fitar da su daga gasar cin kofin Duniya a Qatar cikin watan Disamba, ya ce rataye takalmin nasa shi ne zabi mafi sauki a halin da ya ke ciki.

Tuni dai Chelsea ta wallafa sakon jinjina da bankwana ga tauraron wanda ta bayyana a sahun zakakuran ‘yan wasa da duniya ta gani.

Yayin zaman shi a Real Madrid, Hazard duk da cewa kwallaye 7 kadai ya iya zurawa a wasanni 76 da ya doka amma ya lashe kofin zakarun Turai, da Club World Cup kana European Super Cup da La Liga guda biyu sai kuma Copa del Rey da kuma kofunan Spanish Super Cup guda biyu.

Eden Hazard ya faro wasannin shi a matsayin kwararre da kungiyar kwallon kafa ta Lille da ke Faransa wadda ya zura kwallaye 50 a wasanni 149 yayinda ya taimakawa kungiyar wajen lashe kofin Ligue 1 guda biyu da kuma Coupe de France.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.