Isa ga babban shafi
Wasanni-Kwallon Kafa

Arsenal na zawarcin Eden Hazard daga Real Madrid

Kungiyar kwallon kafa ta Arsenal na shirin fara tattaunawa da Real Madrid ta Spain don sayen dan wasanta na gaba Eden Hazard, a wani yunkuri na magancewa matsalar 'yan wasan gaba da kungiyar ke shirin yi, dai dai lokacin da dan wasan na Belgium ya gaza bayar da gudunmawa a La Liga.

Dan wasan Belhium da ke taka leda da Real Madrid ta Spain Eden Hazard.
Dan wasan Belhium da ke taka leda da Real Madrid ta Spain Eden Hazard. © REUTERS/Sergio Perez
Talla

Tsohon dan wasan na Chelsea mai shekaru 31 ya gaza bayar da gudunmawar da aka yi hasashen zai bayar a Real Madrid tun bayan sayensa a kakar wasa ta 2018 kan yuro miliyan 88 da rabi.

Zuwa yanzu wasanni 65 kadai ya dokawa Madrid a tsawon shekara 2 da rabi da ya shafe a kungiyar mai doka gasar La Liga.

Wasu rahotanni da jaridun wasannin Faransa suka wallafa sun ce Arsenal na shirin tayin tsohon tauraron na Chelsea da ya dage kofunan firimiya biyu, sai dai Hazard dan Belgium na da sauran shekaru 2 da rabi a kwantiragin shekaru 5 da ya kulla da Madrid A 2018.

Hazard lamba 7 a Madrid, baya cikin ‘yan wasa na gaba gaba da Carlo Ancelotti ke amfani da su a wasanni kungiyar na baya-bayan nan.

A bangare guda Arsenal na son sayen Hazard ne don cike gibin da Pierre-Emeric Aubameyang ya haifar mata bayan raba gari da kungiyar zuwa Barcelona.  

Wasu bayanai na cewa baya ga Arsenal akwai kuma kungiyar kwallon kafa ta Newcastle United da ke zawarcin Hazard.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.