Isa ga babban shafi

Poland ta sallami tsohon kocin Portugal da ta dauka aikin horarwa

Poland ta sanar da korar mai horar da tawagar kwallon kafar kasar Fernando Santos daga bakin aikinsa, bayan jagorantar wasanni 6 kacal, kuma a wa’adin kasa da shekara guda tun bayan nadashi mukamin.

Tsohon kocin na Portugal Fernando Santos da ya koma aikin horar da Poland ya rasa aikin nasa ne bayan jagorantar wasanni 6 kacal.
Tsohon kocin na Portugal Fernando Santos da ya koma aikin horar da Poland ya rasa aikin nasa ne bayan jagorantar wasanni 6 kacal. AP - Manu Fernandez
Talla

Wannan kora ta Santos na zuwa ne bayan shan kayen Poland da kwallaye 2 da nema a hannun Albania yayin haduwarsu ta ranar lahadi a wasannin neman gurbin shiga gasar euro2024.

Yanzu haka dai Poland ta koma matsayin ta hudu a rukuninta na wasannin neman gurbin shiga gasar ta EURO inda ta ke shirin karawa da Faroe Island cikin wata mai kamawa bisa fargabar ta iya rasa gurbi a gasar ta badi.

Kafin fara aikin horar da Poland, Santos mai shekaru 68 ya na jagorancin tawagar kasar shi ne Portugal kuma shi ne ma ya kai su ga nasarar lashe gasar ta Euro a 2016 da Nations League a 2019 amma kuma ya ajje aiki bayan gasar cin kofin duniya ta 2022 a Qatar.

Hukumar kwallon kafar Poland a sakon korar ta Santos, ta gode masa game gudunmawar da ya bayar a tsawon lokacin da ya dauka ya na jan ragamar tawagar kasar.

Nasara daya tilo da Santos ya jagoranci Poland ita ce lallasa Jamus da kwallo 1 mai ban haushi a wasan sada zumuntar da suka doka cikin watan Yunin da ya gabata.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.