Isa ga babban shafi

Marciniak ɗan ƙasar Poland ne zai yi alkalancin wasan karshe a Qatar

Hukumar kwallon kafar duniya FIFA ta sanar da Alkalin wasan kasar Poland Szymon Marciniak amastayin wanda zai jagoranci wasan karshe na gasar cin kofin duniya na Qatar da za a yi ranar Lahadi tsakanin Faransa da Argentina.

Alkalin wasa dan kasar Poland Szymon Marciniak shi zai jagoranci wasan karshe na gasar cin kofin duniya na Qatar da za a yi ranar Lahadi 18/12/22 tsakanin Faransa da Argentina.
Alkalin wasa dan kasar Poland Szymon Marciniak shi zai jagoranci wasan karshe na gasar cin kofin duniya na Qatar da za a yi ranar Lahadi 18/12/22 tsakanin Faransa da Argentina. AP - Rui Vieira
Talla

Marciniak mai shekaru 41, ya jagoranci wasannin kungiyoyin biyu a cikin wannan gasa ta Qatar – shi yayi alkalancin wasan da Argentina ta yi nasara a kan Ostireliya a zagayen ‘yan 16 da kuma nasarar da Faransa ta yi a matakin rukuni a kan Denmark.

‘Yan kasar sa biyu Pawel Sokol-nicki da Tomasz List-kiewicz ne zasu taimaka masa alkalanci a wasan na karshe ranar Lahadi mai zuwa.

Dukkansu sun taba jagorantar wasanni a gasar cin kofin duniya na 'yan kasa da shekaru 18 da kuma gasar Euro a shekarar 2016.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.