Isa ga babban shafi

Lewandowski ya yi barin fenariti a wasan Poland da Mexico

Robert Lewandowski ya yi barin bugun daga kai sai mai tsaron raga a wasan da Mexico ta rike su canjaras karkashin wasannin gasar cin kofin duniya ta shekarar 2022 da ke gudana a Qatar.

Robert Lewandowski ne dan wasa na farko da ya barar da fenariti a gasar cin kofin Duniya ta wannan karon.
Robert Lewandowski ne dan wasa na farko da ya barar da fenariti a gasar cin kofin Duniya ta wannan karon. © AFP - GLYN KIRK
Talla

Lewandowski wanda shi ne kyaftin din kasar Poland har zuwa yanzu bai taba cin kwallo a gasar cin kofin duniya ba, kuma zai ci gaba da neman saka kwallo a raga a wannan gasa sakamakon tare kwallonsa da mai tsaron ragar Guillermo Ochoa ya yi.

Filin wasan mai daukar ‘yan kallo dubu 40 ya cika ya batse da akasari magoya bayan Mexico da suka yi ta ihu a lokacin da Lewandowsky ya baras da wannan bugun fenariti.

Haka aka kammala wannan wasa canjaras, duk kuwa da mabanbantan farmakin da bangarorin biyu su suka yi ta kai wa.

Shi ma mai tsaron ragar Poland, Wojciech Szczesny ya yi rawar gani wajen kare martabar kasarsa, a lokacin da Alexis Vega ya kai mai wani farmaki daga kwallon da Jorge Sanchez ya kawo mai.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.