Isa ga babban shafi

Kocin Portugal ya caccaki Ronaldo kan yadda ya fusata bayan sauya shi a wasa

Kocin Portugal,  Fernando Santos ya caccaki Cristiano Ronaldo a  kan halin da ya nuna baya da aka sauya shi daga wasan Portugal da Korea ta Kudu a ranar Juma’a, kuma bai bada tabbacin ko dan wasan zai buga wasansu da Switzerland a yau Talata.

Cristiano Ronaldo.
Cristiano Ronaldo. AP - Darko Bandic
Talla

Fuskar Ronaldo ta nuna ya fusata a lokacin da aka sauya shi daga wasan a minti na 65 a wasan da suka sha kashi 2-1, inda kamarori suka yi ta nuna fuskar dan wasan mai shekaru 37 cikin yanayi na gunaguni.

Bayan haka Ronaldo ya shiga musayar kalamai  cikin fushi da wani dan wasan Korea, wato Cho Gue-Sung a yayin da yake barin filin wasa, kuma bayan wasan ne kocin ya gano yadda Ronaldo ya karbi sauya shi da aka yi.

Kocin ya kalli bidiyon, kuma bai ji dadin abin da Roanldo ya yi ba, inda ya ce baya kusa da inda lamarin ya auku ballantana ya ji abin ya ce, shi dai abin da ke gabannsa yanzu shine wasa na gaba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.