Isa ga babban shafi

Spain ta lashe kofin Nations League bayan doke Croatia a finareti

Dani Carvajal ya taimakawa Spain lashe gasar Nations League bayan doke Croatia a bugun fanariti da ci 5 - 4 a wasan da suka fafata ranar Lahadi.

'Yan wasan tawagar Spain lokacin da suka lashe gasar Nations League bayan doke Crotia a bugun finareti.18/06/23.
'Yan wasan tawagar Spain lokacin da suka lashe gasar Nations League bayan doke Crotia a bugun finareti.18/06/23. AP - Martin Meissner
Talla

An doka mintuna 90 da kuma karin lokaci amma babu ci har sai da aka je bugun daga kai sai tsaron raga, nan ne Golan Spain Unai Simon ya nuna bajintar sa wajen tare kwallaye Lovro Mayer da Bruno Petkovic, kafin Carvajal ya zura kwallo na karshe da ya baiwa tawagar La Roja nasarar lashe kofin su na farko tun bayan gasar Euro 2012, tare da dakushe fatan Croatia na dage kofin.

'Yan wasan tawagar Spain lokacin da suka lashe gasar Nations League bayan doke Crotia a bugun finareti.18/06/23.
'Yan wasan tawagar Spain lokacin da suka lashe gasar Nations League bayan doke Crotia a bugun finareti.18/06/23. AP - Peter Dejong

Tawagar Zlatko Dalic, da ta yi na biyu a gasar cin kofin duniya a shekarar 2018, ta kuma yi na uku a shekarar 2022 a Qatar, ba ta taba lashe wani babban kofi ba, sai dai ta yi fatan samun nasarar lashe gasar Nations League ta bana, da zata kara wa kyaftin din ta Luka Modric da ya buga wasansa na 166 daraja.

'Yan wasan tawagar Crotia lokacin da suka sha kashi a hannun Spain a gasar Nations League a bugun finareti.18/06/23.
'Yan wasan tawagar Crotia lokacin da suka sha kashi a hannun Spain a gasar Nations League a bugun finareti.18/06/23. AP - Peter Dejong

Nasarar wata kwarin guiwa ce ga sabon kocin Spain Luis de la Fuente bayan da ya fuskanci kakkausar suka a watan Maris sakamakon doke su da Scotland ta yi a wasan neman gurbin shiga gasar cin kofin Turai na 2024. Haka kuma tamkar ramuwar gayyace kan dokar da Faransa ta yi musu a wasan karshe na 2021.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.