Isa ga babban shafi

Super Eagles ta rikito zuwa matsayi na 40 a duniya a jadawalin FIFA

Tawagar Najeriya ta fuskanci komawa baya da matsayi biyar a jadawalin FIFA na Maza a watan Fabrairu.Super Eagles, wacce ta kasance ta 35 a duniya a jadawalin da aka fitar a watan Disamba, ta rage maki 14 zuwa mataki na 40.

Tawagar 'yan wasan Najeriya ta Super Eagles
Tawagar 'yan wasan Najeriya ta Super Eagles REUTERS/Dylan Martine
Talla

Koma bayan da Eagles ta fuskanta ya samo asali ne saboda rashin tabuka abin kirki da su ka yi a wasan neman tikitin shiga gasar cin kofin Afrika da suka yi da kasar Guinea-Bissau mara karsashi sosai a sabgar tamola a cikin watan da ake nazarin bada makin.

Wild Dogs sun yi galaba a kan ‘yan wasan Super Eagles a wasan farko cikin karawa biyu a filin wasa na Moshood Abiola da ke Abuja kafin su rama da ci 1-0 a Bissau a wasa na biyu.

A jadawalin matakin na maza da FIFA ta fitar ranar 22 ga watan Disambar, 2022 Eagles ta kammala a matsayi na 35, sun sauka da mataki daya a lokacin. A Afirka Najeriya ta rikito zuwa na 6.

Morocco ta daya a Afirka

Morocco ta ci gaba da zama ta daya a nahiyar kuma ta 11 a duniya. Sai kuma Senegal mai matsayi na biyu, wacce ita ma ta koma na 18 a duniya.

Tunisiya ta ci gaba da rike matsayinta na uku a Afirka kuma ta 28 a duniya, yayin da Algeria ta sha gaban Masar ta zama ta hudu a Afirka yayin da ta kara mataki 6 zuwa matsayi na 34. Masar wadda ta kasance ta 39 a matsayi na baya-bayan nan, ta kaka mataki hudu inda ta zama ta 35 a duniya sannan ta biyar a Afirka.

Najeriya da Kamaru da Ivory Coast da Mali da Ghana na cikin kasashe 10 na farko a Afirka.

Argentina ta daya a duniya

Kasar Argentina da ta lashe gasar cin kofin duniya ta sake komawa saman teburin jadawalin a karon farko cikin shekaru shida.

Tawagar Lionel Scaloni - wacce ta lashe kofin duniya na uku da nasara mai ban sha'awa a wasan karshe da Faransa a Qatar a bara - ta samu nasara a wasannin sada zumunta da Panama da Curacao a watan Maris.

Argentina ta maye gurbin abokiyar hamayyarta Brazil a, bayan da Selecao ta yi rashin nasara a wasan sada zumunci da Morocco wadda ta kai wasan dab da na kusa da karshe a gasar cin kofin duniya a watan Maris, abin da ya sa ta koma mataki na uku.

Faransa ta biyu

Faransa ce ta biyu bayan da ta doke Netherlands da Jamhuriyar Ireland a gasar neman cancantar shiga gasar Euro 2024 yayin da Selecao ta koma matsayi na uku.

Belgium, Ingila, Netherlands, Croatia, Italiya, Portugal, da Spain ne ke cikin goma.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.