Isa ga babban shafi

Super Eagles ta Najeriya ta zama ta 15 a kungiyoyi mafi daraja a duniya

Duk da rashin samun damar zuwa gasar cin kofin duniya da ake gudana a kasar Qatar, darajar Super Eagles ta Najeriya ta tashi a bangaren da suka shafi hada-hadar kudade.

Magoya bayan tawagar Super Eagles ta Najeriya a filiin wasa na Lagos. 2013
Magoya bayan tawagar Super Eagles ta Najeriya a filiin wasa na Lagos. 2013 AP - Sunday Alamba
Talla

Kungiyar kwallon kafar Najeriya da ta zama zakaran Afirka har sau uku ta kasance a matsayi na 15 a jerin kungiyoyin kasa da kasa da suka fi kima a duniya, yayin da kuma ta tashi daga matsayi na uku a Afirka zuwa  mafi daraja a nahiyar.

Eagles dai na samun tagomashi ne da ‘yan wasan da ke taka leda a gasar lig-lig na Turai, wanda hakan ya sanya su zama cikin kungiyoyi mafi daraja a duniya, da jimillar kudin da ya kai €303.35m.

A watan Oktoba, an sanya su a matsayi na 21 tare da darajar kasuwa na € 256.65m.

Tsoffin 'yan wasan Super Eagles da ake kira Green Eagle
Tsoffin 'yan wasan Super Eagles da ake kira Green Eagle The Guardian

A halin da ake ciki Darajar ‘yan wasan Najeriya ta samu karin Yuro miliyan 46.7 idan aka kwatanta da darajar ‘yan wasan a baya.

Farashin wasu  ‘yan wasan na Eagles, ya tashi a kasuwannin hada-hadar ‘yan wasa,  biyo bayan bajintar da suke nunawa a kungiyoyinsu daban-daban a baya-bayan nan.

Victor Osimhen ya daga darajar Najeriya

Mafi girma daga cikinsu shine dan wasan gaba na Napoli, Victor Osimhen, wanda a cewar transfermarkt, ya fi samun ta yi mafi girma tsakanin watan Satumba da Oktoba.

Saboda zaren da yake ja yanzu haka darajar dan wasan na Napoli ya karu da Yuro miliyan 10 a kasuwanni, inda ya tashi daga €65m zuwa €70m, kuma yanzu haka shine dan wasan Najeriya mafi daraja.

Victor Osimhen
Victor Osimhen © REUTERS/Mohamed Abd El Ghany

Ko da yake dan wasan tsakiya na Leicester City, Wilfred Ndidi, ya samu raguwar Yuro miliyan 20 a cefane sa saboda lokutan da ya yi fama da jinya , ya kasance dan wasa na biyu mafi daraja a kungiyar da Yuro miliyan 40, idan aka kwatanta da darajarsa na €60m a baya.

Dan wasan gaba na Atalanta, Ademola Lookman, wani dan wasa ne wanda ya ba da gudummawa a darajar kasuwar Super Eagles yayin da ya tashi daga darajarsa ta farko na € 10m zuwa € 20m, bayan rawar gani da ya nuna a kulob din Italiya.

Dan wasan gaba na Everton, Alex Iwobi, shi ma ya samu karuwar darajar sa yayin da ya tashi daga €22m zuwa €25m.

Sauran 'yan wasa da suka daga darajar Najeriya

Yayin da darajar kasuwar Samuel Chukwueze ta kasance a kan Yuro miliyan 20, sauran ’yan wasa kamar su Terem Moffi, Joe Aribo da Calvin Bassey duk sun ba da gudummawar ci gaban darajar kungiyar da jummalar darajar €48m.

Tun bayan da ya kai darajar Miliyan 1 a rayuwarsa na kwallo lokacin da ya tashi daga Yuro 900,000, mai tsaron raga Maduka Okoye ya ci gaba da samun ci gaba  darajarsa duk da karancin fitowa tun bayan komawarsa  Watford. Yanzu haka darajar mai tsaron ragar ya kai €2.5m.

Dan wasa mai tsaron bayan Najeriya Maduka Okoye
Dan wasa mai tsaron bayan Najeriya Maduka Okoye © Maduka Okoye twitter

Ndidi ba shine kawai dan wasan da ya samu raguwar tayin kudi ba, dan wasan gaba Genk da Paul Onuachu, sun samu raguwar  Yuro miliyan 7.  Yanzu yana karbar Yuro miliyan 15 idan aka kwatanta da cefanen €22m.

Najeriya ta zarta Senegal

Kafin fitar da wannan sabon matsayi, Senegal, wacce a baya ita ce ta fi kowace kungiya daraja a nahiyar Afirka, kuma ta 14 a duniya da darajarsu ta kai Yuro miliyan 321.40, yanzu ita ce ta hudu a Afirka kuma ta 24 a duniya da darajar kungiyar ta kai Yuro miliyan 229.50.

Ivory Coast ce ta biyu a Afirka kuma ta 19 a duniya tana da darajar kasuwan Yuro miliyan 259, yayin da Morocco da Ghana ke matsayi na uku da na biyar.

Har yanzu Ingila ke kan gaba

A halin da ake ciki, Ingila ta samu karuwar Yuro miliyan 12, inda ta ci gaba da kasancewa kungiyar da ta fi kowacce daraja a duniya da kasuwar Yuro biliyan 1.26, yayin da Brazil da Faransa suka mamaye matsayi na biyu da na uku da darajar kasuwar €1.14bn da €1.03bn bi da bi.

Portugal da Jamus ke rike da matsayi na biyar da Yuro miliyan 937.00 da kuma €885.50m.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.