Arsenal ta amince da tayin Napoli na Yuro miliyan 100 kan Osimhen
Arsenal na shirin amincewa da tayin sayin dan wasan Napoli Victor Osimhen na Yuro miliyan 100, bayan da kulob din na Italiya ya ki amincewa da tayin farko na Euro miliyan 60 a ranar Litinin.
Wallafawa ranar:
Cinikin dan wasa mafi tsada da Gunners ta yi a baya shi ne lokacin da ta fanshi Nicolas Pepe daga Lile na kasar Faransa a shekarar 2019 kan fam miliyan 72.
A cewar jaridar Italiya, La Gazzetta dello Sport, Arsenal na son siyan dan wasan na Najeriya mai shekaru 23 a matsayin wanda zai maye gurbin tsohon kyaftin dinta Alexander Lacazette, wanda ya koma Lyon kyauta a bana.
"Arsenal na shirin shiga tattaunawa da Napoli don sayen Osimhen wanda ake bukatan Yuro miliyan 100 a kansa. Ita ma Manchester United ta nuna sha'awar dan wasan, amma Gunners na neman yi mata fintinkau.
Dan wasan wanda ya zura kwallaye 18 kuma ya taimaka a wasanni 32 a kakar wasan da ta wuce, kungiyoyi Turai da dama na sa’ido a kansa.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu