Isa ga babban shafi

Napoli ta kara farashin Osimhen zuwa euro miliyan 120

Kungiyar Napoli dake gasar Seria A ta kara yawan kudin da za ta bukaci a biya ta kan dan wasanta na gaba, dan asalin Najeriya wato Victor Osimhen.

Dan wasan gaba na kungiyar Napoli Victor Osimhen.
Dan wasan gaba na kungiyar Napoli Victor Osimhen. REUTERS - CIRO DE LUCA
Talla

Wasu majiyoyi daga kungiyar ta Napoli sun ce karin farashin Osimhen daga euro miliyan 100 zuwa euro miliyan 120 ya biyo bayan tayin da wasu kungiyoyi suka fara gabatar mata kan neman kulla yarjejeniya da dan wasan a baya bayan nan.

Kungiyoyin da suka fara zawarcin sauyin shekar matashin dan wasan mai shekaru 23 daga Najeriya dai sun hada da Tottenham, Arsenal, Barcelona, Real Madrid da kuma Newcastle.

Yanzu haka dai Victor Osimhen na daga cikin ‘yan wasan gaba mafi kwarewa a gasar Seria A ta Italiya inda a kakar wasa ta bana ya ci wa Napoli kwallaye 11 daga cikin wasanni 20 da ya buga.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.