Isa ga babban shafi
Wasanni

Napoli na shirin hana Osimhen shiga gasar AFCON mai zawa

Napoli na shirin dakatar da dan wasan Super Eagles Victor Osimhen da sauran 'yan wasan Afirka daga buga gasar cin kofin Afirka ta 2021 a watan Janairu mai zuwa a Kamaru.

Dan wasan Najeriya da Napoli Victor Osimhen's lokacin da ya bude gasar Serie A da kwallo
Dan wasan Najeriya da Napoli Victor Osimhen's lokacin da ya bude gasar Serie A da kwallo Carlo Hermann AFP
Talla

A cewar jaridar Corriere dello Sport, Lauyoyin Napoli suna nazarin yuwuwar toshe manyan taurarin na Afirka ciki har da Osimhen daga wasannin na AFCON a shekara mai zuwa.

Napoli tana da 'yan Afirka guda uku bayaga Osimhen, ciki harda Zambo Anguissa dake tawagar Kamaru mai masaukin baki, sai kuma Kalidou Koulibaly na Senegal da Adam Ounas, Ghoulam na Algeria.

AFCON wanda aka shirya gudanarwa a shekarar 2021 an canza shi zuwa 9 ga watan Janairu zuwa 6 ga Fabrairu, 2022 saboda barkewar COVID-19.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.