Isa ga babban shafi

Kun san dan wasan tawagar Jamus da ya zabi taka leda a Najeriya?

Dan wasan baya na kungiyar Hoffenheim Kevin Akpoguma wanda yanzu haka ke filin atisaye da tawagar Super Eagles ta Najeriya a Austria, yace zai koyi rera taken Najeriya kafin wasar sada zumunta da kasar zata kara da Algeria.

Kevin Akpoguma dan wasan Jamus da ya kaura zuwa tawagar Najeriya bayan amincewar FIFA
Kevin Akpoguma dan wasan Jamus da ya kaura zuwa tawagar Najeriya bayan amincewar FIFA Bundesliga
Talla

Tsohon kyaftin din kungiyar kwallon kafa Jamus na ‘yan kasa da shekaru 20, wanda mahaifinsa dan Najeriya ne yayin da mahaifiyarsa Bajamushe, kuma haifeffen kasar Jamus ya zabi ya takawa Najeriya leda.

Kuma burin na sa ya cika ne bayan da Hukumar Kwallon kafa ta Duniya FIFA ta amince dan wasan ya kaura daga tawagaJamus wasa don fafatawa a Super Eagles.

A bangare daya, Kungiyar kwallon kafa ta Najeriya Super Eagles, tace da yardar Allah zata kawo karshen tarihin Cocin Algeria Djamel Belmadi, wanda ba a taba doke shi ba tun da ya fara haror da kungiyar a shekarar 2018.

Takwaransa na Super Eagles, Gernot Rohr, ya bayyana wanna fatan doke Algeria, a karawar sada zumunta da kungiyoyin biyu zasuyi ranar jumma’a a kasar Austria.

Algeria ta buga wasanni har 18 ba tare da rashin nasara, wanda 14 daga cikin wasannin Belmadi ke jagoranta. Desert Foxes sun ci wasanni 12 kuma sun yi canjaras 2 karkashinsa, tun bayan da ya karbi ragamar kungiyar a shekarar 2018.

Algeria dake arewacin Afirka ta doke Najeriya da ci 2-1 a wasan kusa da na karshe na Gasar cin Kofin Afirka a shekarar 2019 a Masar, inda suka doke Senegal da ci daya mai ban haushi a wasan karshe kuma saka dauki kofin karon farko cikin shekaru 29.

To sai dai Najeriya ba kanwa lasa bace ga Algeriar, domin cikin wasanni 25 da suka fafata tsakaninsu Najeriya ta lashe 9, yayin da ta doke ta 8 sannan suka tashi canjaras sau takwas.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.