Super Eagles ta rikito zuwa ta 5 daga ta 3 a sabon jadawalin FIFA
Tawagar kwallon kafar Najeriya ta Super Eagles ta rikito zuwa matsayin ta 5 a Afrika daga ta 3 da ta ke a baya cikin sabon jadawalin kasashe mafiya iya kwallo da hukumar kwallon kafa ta Duniya FIFA ta fitar.
Wallafawa ranar:
Sabon jadawalin da FIFA ta fitar ya nuna yadda Super Eagles ta koma matsayin ta 35 a matakin Duniya daga ta 32 da take a baya wanda ke da nasaba da rashin nasarrata a wasannin sada zumuntar da ta doka a baya-bayan.
Brazil ta ci gaba da zama da 1 a jadawalin na FIFA biye da Argentina a matsayin ta 2 bayan nasararta ta lashe kofin Duniya kana Faransa a matsayin ta 3 sai Belgium ta 4 tukuna Ingila matsayin ta 5.
Matakin rikitowar ta Super Eagles na da nasaba da rashin nasararta ta iya zuwa gasar cin kofin Duniya da ta gudana a Qatar bayan shan kaye a hannun Ghana cikin watan Maris din shekarar nan.
Morocco ta shiga gaban Senegal inda ta koma matsayin ta 1 a Afrika yayinda Senegal wadda ta jima a wannan gurbi yanzu haka ta koma ta 2 kana sai Tunusia ta 3 yayinda Kamaru ta koma ta 4.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu