Isa ga babban shafi

Super Eagles ta yi asarar naira biliyan 4 saboda gaza zuwa gasar cin kofin Duniya

Babbar tawagar kwallon kafar Najeriya, Super Eagles ta rasa damar samun tsabar kudi har Naira biliyan 4 da rabi sakamakon gaza samun tikitin shigaa gasar cin kofin duniya ta shekarar 2022 da za ta gudana a Qatar.

Kungiyar kwallon kafar Super Eagles ta Najeriya
Kungiyar kwallon kafar Super Eagles ta Najeriya © AP - Sunday Alamba
Talla

Super Eagles dai ta rasa damar zuwa gasar cin kofin duniyar ne sakamakon shan kayenta a hannun Ghana har gida yayin wasan da bangarorin biyu suka doka a babban birin Najeriya Abuja. 

Kwallon da Thomas Partey ya ci ce ta taka wa Najeriya birki, wanda ya kai ta ga tafka irin wannan asara, kuma duk da cewa William Troost Ekong ya ci wata kwallo, ba ta kara wa Najeriya komai.

A wannan karon ma hukumar kwallon kafa ta duniya, wadda ba ta yi kasa a gwiwa wajen bada tukuici ga duk  tawagar da ta shiga gasar ba, za ta bayar da dala miliyan 440 ga kowace tawaga, wadda ta yi dai dai da biliyan 4 da rabi na Nairar Najeriya.

A watan Nuwamba mai kamawa ne za a faro gasar a kuma karkare a watan Disamba, gasar da kasashe 32 karkashin rukunnai 8 za su fafata da juna, yayinda Faransa mai rike da kambu za ta yi kokarin kare kofin gasar wanda ta lashe a 2018.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.