Al-Hilal na Saudiya ta yi wa Messi tayin sama da Yuro miliyan 400 duk shekara
Kungiyar Al-Hilal ta kasar Saudiya ta yi tayin baiwa fitaccen dan wasan kasar Argentina, Lionel Messi, Yuro miliyan 400 a shekara.
Wallafawa ranar:
Masanin harkokin hada-hadar ‘yan wasan kwallon kafa Fabrizio Romano ne ya tabbatar da hakan a daren Talata.
A cewarsa, albashin da akayi wa Messi tayi ya haura dala miliyan 438 a duk shekara.
Sai dai ana ganin Messi na sha'awar ci gaba da taka leda a Turai, inda tsohuwar kungiyarsa Barcelona ke fatan ganin yayi mata kome .
Haduwar Hamayya
Idan a karshe Messi ya amince da tayin daga Al Hilal, zai sake sabunta fafatawa da Cristiano Ronaldo wanda tuni ya ci wa Al Nassr kwallaye 10 a gasar da Saudiya.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu