Isa ga babban shafi

Barcelona na son maido da Lionel Messi

Barcelona ta tuntubi Lionel Messi game da yi wa kungiyar kome kamar yadda mataimakin shugaban kungiyar Rafeal Yuste ya bayyana.  

Lionel Messi.
Lionel Messi. © LUSA - MIGUEL A. LOPES
Talla

Messi mai shekaru 35, shi ne dan wasa mafi yawan kwallaye a tarihin Barcelona, inda ya ci mata kwallaye 672 a cikin wasanni 778 da ya buga mata.

A shekarar 2021 ne, ya raba gari da Barcelona bisa dalilai na tsuke bakin aljihun  kungiyar, inda ya koma PSG ta Faransa. 

Kwantiragin Messi da PSG zai kare a cikin wannan kakar kuma bayanai na cewa, ya fi sha’awar ci gaba da zama a kungiyar ta Farasansa. 

Shekaru biyu da suka gabata, Messi ya amince ya kulla sabuwar yarjejeniya da Barcelona wadda ta kunshi zabtare masa albashi, amma dai hakan bai yiwu ba. 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.