Isa ga babban shafi

Ronaldo ya sha naushi a fuska a wasansa da Messi

Christiano Ronaldo ya sha naushi a fuska, amma duk da haka ya  jefa kwallaye biyu a wasan sada zumunta da sabuwar kungiyarsa ta Al Nassr ta yi da PSG a birnin Riyadh na Saudiya a yau.

Cristiano Ronaldo da Lionel Messi
Cristiano Ronaldo da Lionel Messi © Arabian Business
Talla

Mai tsaren ragar PSG, Keylor Nava, shi ne ya naushi Ronaldo da dungulalliyaar hannu, lamarin ya sa alkali ya ba shi bugun fanariti wanda Ronaldo din ya zura a raga.

Koda yake PSG ce ta  samu nasara da kwallaye 5-4 a wasan wanda ya sake hada Ronaldo da tsohon abokin hamayyarsa a duniyar tamola, wato Lionel Messi na PSG.

Messi da Kylian Mbappe dukkaninsu sun jefa kwallo a raga a yayin fafatawar, yayin da Neymar ya barar da bugun fanariti.

Daga cikin ‘yan kallo da suka halarci filin wasan na Sarki Fahad mai daukar nauyin mutane dubu 69, har da wani attajirin Saudiya mai rikunin gidaje da ya biya Dala miliyan 2.6 domin sayen tikitin kallon wasan kai tsaye.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.