Isa ga babban shafi

Messi ya zura kwallo ta 800 bayan nasarar Argentina kan Panama

Lionel Messi ya zura kwallo mai kayatarwa a wasan sada zumuntar da ya gudana tsakanin Argentina da Panama jiya alhamís wanda aka tashi wasa 2 da nema a birnin Buenos Aires.

 Lionel Messi.
Lionel Messi. REUTERS - CARL RECINE
Talla

Messi mai shekaru 35 da ya lashe kyautar Ballon d’Or 7 ya zura kwallon ne a bugun tazarar da Argentina ta samu gab da karkare wasa bayan kwallon da matashi Thiago Almada ya zura tun a mintuna farko na wasan.

Kwallon ta jiya dai ta zama kwallo ta 800 da Messi ya zura tun daga fara taka ledarsa zuwa yanzu kuma bayan zura kwallon anga yadda gabakidaya filin wasan ya dau sowa yayinda aka rika wasa da tartsatsin wuta wadanda ke fitar da sunan Messi a jiki.

Akalla mutane miliyan 1 da rabi ne suka nemi shiga filin wasan mai daukar mutum dubu 83 amma kuma hukumomi suka dakile su wanda ya tilasta musu kallon wasan a akwatunan haska wasa na kan tituna.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.