Isa ga babban shafi

Lionel Messi ba zai samu bugawa kungiyarsa ta PSG wasa ba a gasar Lique 1

Tauraron ‘dan wasan duniya Lionel Messi ba zai samu bugawa kungiyarsa ta PSG wasa ba a gasar Lique 1 ta Faransa da za suyi da Monaco ba, saboda raunin da ya samu a cinyarsa, abinda ke bayyana fargabar cewar watakila ba zai iya buga karawar da kungiyarsa za tayi da Bayern Munich a gasar cin kofin zakarun Turai na makon gobe ba.

 Lionel Messi, Dan wasan PSG
Lionel Messi, Dan wasan PSG REUTERS - KAI PFAFFENBACH
Talla

Kungiyar PSG ta sanar da cewar kaftin din na kasar Argentina ya samu rauni a karawar da suka yi da Olympique Marseille ranar Laraba, wadda suka samu nasara da ci 2-1. 

Sai dai kungiyar tace tana fatar ganin Messi ya koma atisaye ranar litinin bayan liitoci sun duba lafiyarsa, sun kuma tabbatar da cewar baya fuskantar wani hadari. 

Mai horar da ‘yan wasan PSG Christophe Galtier yayi watsi da fargabar da ake cewar Messi ba zai iya shiga karawar da za suyi da Bayern Munich ba. 

Galtier yace duk da yake Messi ba zai shiga karawar Monaco ba, za’a fafata da Bayern Munich tare da shi saboda muhimmancinsa. 

Yanzu haka abokin wasansa Kylian Mbappe na fama da raunin da ba zai shiga karawar guda biyu ta Monaco da Bayern Munich ba. 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.