Isa ga babban shafi

Serena za ta sauya matsaya a yunkurinta na ritaya daga fagen Tennis

Serena Williams ta bayyana yiwuwar komawa fagen wasan kwallon tennis, kwanaki kadan bayan da ta sanar da kawo karshen wasan da ta shafe shekaru fiye da 20 ta na haskawa a cikinta.

Serena Williams bayan ficewa daga gasar Canadian Open cikin watan jiya.
Serena Williams bayan ficewa daga gasar Canadian Open cikin watan jiya. AFP
Talla

A gasar US Open da ta gabata ne, Williams ta sanar da yin bankwana da fagen na Tennis, wadda ta zama mace ta biyu a duniya mafi girma a cikinta, bayan lashe kofunan gasar Grand Slam 23, inda take biye da fitacciyar 'yar wasan tennis ta Australia Margaret Court, mai kofuna 24.

Sai dai a halin yanzu Serena Williams ta fara duba yiwuwar komawa fagen kwallon na Tennis, inda ta bayyana cewa yayarta Venus Williams ke matsa mata lambar janye ritayar da ta yi.

Venus da Serena sun shafe tsawon shekaru suna haskawa a fagen na Tennis tare da lashe manyan gasa, sai dai a baya-bayan nan suna ganin shan kaye a hannun kananun yara sabbin hannu a wasan na Tennis.

Fiye da shekaru 2 kenan, rabon da Serena ta yi wata gagarumar nasara a fagen na Tennis inda ko a baya-bayan nan ta yi rashin nasara a hannun Belinda dalilin da ya tilasta mata barin Canada tun a zagayen farko.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.