Isa ga babban shafi

Serena Williams ta yi watsi da batun yin ritaya daga kwallon tennis

Serena Williams ta yi watsi da batun yin ritaya daga wasan kwallon tennis, inda a baya bayan nan ta nanata cewa tana da sha'awar fafatawa a gasar US Open nan gaba a wannan shekara, duk da rashin nasara ta ban mamaki da ta sha a gasar Wimbledon dake gudana a Ingila.

Serena Williams.
Serena Williams. AFP
Talla

Yayin ganawa da manema labarai, Serena ta tunatar da cewa gasar US Open, ita ce babbar gasar kwallon tennis ta Grand Slam ta farko da ta lashe dan haka tana da muhimmanci a gareta, kuma shigarta a bana kwarin gwiwa zai kara mata, bayan kayen da ta sha a Wimbledon.

Fitacciyar ‘yar Tennis din mai shekaru 40 ta yi wannan tsokaci ne bayan da ta sha kashi tun a zagayen farko da 7-5, 1-6, 7/6 da kuma 10/7, yayin karawa da Bafaranshiya Harmony Tan, wadda a yanzu haka ita ‘yar wasa ta 115 a duniya wajen kwarewa a gasar Tennis.

Sau 23 Serena Williams ta lashe kofunan babbar gasar Tennis ta Grand Slam da suka hada da na Wimbledon, French Open, US Open da kuma Australian Open, kofunan da ta taba lashes u jere da juna a tsakanin 2014 zuwa 2015.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.