Isa ga babban shafi

Serena Williams ta yi bankwana da Canada bayan shan kaye a hannun Belinda

Serena Williams ta yi ban kwana da Canada cikin hawaye bayan da ta yi rashin nasara 6-2 da 6-4 a karawar ta da Belinda Bencic a jiya Laraba kwanaki kalilan bayan bayanin tauraruwar ta Tennis da ke cewa ta na daf da yin murabus a harkar kwallon na Tennis.

Cikin shekarar nan sau 4 kadai Serena ta doka manyan wasannin Tennis.
Cikin shekarar nan sau 4 kadai Serena ta doka manyan wasannin Tennis. AP - Kirsty Wigglesworth
Talla

Dama dai an san ‘a rina’, saboda Bencic ‘yar kasar Switzerland, ita ce ke rike da lambar zinariya ta gasar Olympic, a yayin da Serena, mai shekaru 40 tana fafatawa ne a wasanta na 3 kawai a  wannan shekarar ta 2022.

Williams tsohuwar lamba daya ta gasar, ta yi jawabin ban kwana mai sosa zuciya, inda ita kanta ta gaza hana hawaye zuba, duba da cewa akwai yiwuwar ta kawo gabar da za su  yi hannun riga da kwallon tennis.

Williams, wadda za ta cika shekaru 41 a wata mai zuwa ta doke ‘yar kasar Spain, Nuria Parrizas Diaz a ranar Litinin a nasararta ta farko bayan watanni 14.

A shekarar 1999 Williams ta lashe babban kofin Grand Slam na farko ta na da shekaru 17 a gasar US Open, kuma tun daga nan ne tauraruwarta ta fara haskawa yayinda ta mamaye gasar bangaren mata tsawon shekaru.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.