Isa ga babban shafi

Serena da Venus sun yi waje daga gasar US Open a ajin masu karawa bibbiyu

An kawo karshen haskawar fitattun ‘yan wasan tennis kuma ‘yan uwan juna wato Serena da Venus Williams a gasar US Open da ke gudana  ajin masu karawa bibbiyu.

Wasan da Serena da Venus suka sha kaye a hannun Lucie Hradecka da Linda Noskova na jamhuriyar Czech.
Wasan da Serena da Venus suka sha kaye a hannun Lucie Hradecka da Linda Noskova na jamhuriyar Czech. Reuters
Talla

A jiya Alhamis ne dai Yaya da kanwar na kasar Amurka suka fice daga gasar ta US Open tun a zagayen farko, bayan shan kaye a hannun 'yan wasan Czech biyu Lucie Hradecka da Linda Noskova, wadanda suka samu nasara  da 7-6 7/5, da kuma 6-4.

Rabon da  Serena da Venus Williams su yi wasa tare tun shekarar 2018.

'Yan wasan tennis din na Amurka sun lashe kofunan gasar tennis ta Grand Slam har guda 14 da lambobin zinare uku na gasar Olympics yayin awsannin da suka fafata ajin masu karawa bibbiyu.

Tun a shekaran jiya laraba ne, Serena Williams mai shekaru 40 ta shiga zagaye na uku na gasar US Open ajin masu karawa dai-dai inda ta yi galaba a kan Anett Kontaveit ‘yar kasar Estonia.

Fitacciyar 'yar wasan tennis din wadda ta bayyana shirinta na yin ritaya bayan kammala gasar ta US Open ta doke Kontaveit da ci 7-6 (7/4), 6-2, yayin da ita kuma Kontaviet ta samu nasara sau guda kan Serenan da 6-2 gabanin yin waje da ita a jiya alhamis.

Serena ba ta bayyana ranar da za ta sanar da yin ritaya daga fagen na Tennis ba, duk da cewa ta bayyana yiwuwar gasar ta US Open ta zama karshen karawarta a fagen.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.