Isa ga babban shafi

Serena Willians ta dawo fagen daga bayan shafe shekara guda tana hutu

Serena Williams fitacciyar yar wasar tennis daga Amurka  bayan share shekara daya na hutu daga fagen tennis ,ta dawo  da karfin ta a gasar ta Wimbledon,wurin da yar wasar ta lashe kofuna  sau 7.

Serena Williams fitacciyar 'yar wasan Tennis
Serena Williams fitacciyar 'yar wasan Tennis © Pierre Rene-Worms/RFI
Talla

A yau juma’a  Serena Williams za ta fafata da Harmony Tan yar kasar Faransa dake mataki na 113 a jerryn yan wasa a Duniya.

Serena Williams mai shekaru 40 da ta kasance a mataki na farko a Duniyar tennis, ta samu kan ta a mataki na karshe a yanzu haka kamar yada hasashen ya nuna sabili da dogon hutu da ta dauka tun a shekara ta 2021.

Harmony Tan , daga kasar Faransa mai shekaru 24,wannan dai ne karo na farko da wannan yar wasa za ta haska a gasar dake gudana a birnin London.

A daya gefen,yar kasar Fologne dake mataki na farko a jerryn yan wasa a Duniya a fagen Tennis za ta kara da  yar kasar Crotia Jana Fett da ta tsalaka mataki na gaba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.