Isa ga babban shafi

Alcaraz ya zama mafi karanci shekaru da ya haye matsayin lamba 1 a gasar Tennis

Carlos Alcaraz dan kasar Spain ya kafa tarihin zama mafi kankantar shekaru da ya zama lamba daya a fagen gasar Tennis ta duniya.

carlos alcaraz shine mafi karancin shekaru da ya kasance lamba daya a duniya.
carlos alcaraz shine mafi karancin shekaru da ya kasance lamba daya a duniya. AP - Manu Fernandez
Talla

Alcaraz ya yi wannan bajintar ce, bayan lashe kofin gasar US Open yana da shekaru 19, inda a wasan karshen da ya gudana a jiya Lahadi, ya lallasa Casper Ruud dan kasar Norway da 6-4, 7-6 da kuma 6-3, yayin da shi kuma Ruud ya samu nasara sau guda kan Alcaraz da 6-2.

Matasshin dan kasar Spain ya kuma kasance daan wasan tenis mafi karancin shekaru da ya lashe baabban kofin Grand Slam tun bayan da Rafael Nadal ya lashe a shekarar 2005 a gasar French Open.

Tsohon lamba daya, Nadal shine lamb ana 3 a duniya bayan da ya sha kashi a gasar US Open a hanun Ba’amurke Frances Tiafoe.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.