Tennis: Carlos Alcaraz ya lashe gasar Madrid Open
Matashin dan wasan tennis, Carlos Alcaraz ya kammala makon da ya gabata da galaba a kan mai kare kofin babbar gasar Madrid Open Alexander Zverev, inda ya lashe gasar.
Wallafawa ranar:
Dan wasan mai shekaru 19, wanda ya doke Rafael Nadal da Novak Djokovic a wasanninsa 2 da suka gabata, ya lallasa dan kasar Jamus din, wanda ke matsayi na 2 a duniya da ci 6-3 6-1.
Wannan ne kofin gwani na gwanaye da ake kira Masters 1000 na 2 da ya lashe a wannan shekarar bayan Miami Open da ya cinye a watan da ya gabata, kuma kofinsa na 4 a wanna shekarar.
Alcaraz ya shirya tsaf don darewa matsayi na 6 a duniya gabanin gasar French Open nan gaba a watan Mayun an da muke ciki.
Dan wasan ya bayyana gasar a matsayin mai mahimanci a gare shi, inda ya ce ya sha zuwa kallo a lokacin da ya ke yaro mai shekaru 7 zuwa 8.
Alcaraz ya buga wasa babu kama hannun yaro, inda ya zame wa abokin hamayyar tasa, dan kasar Jamus karfen kafa daga farkon wasa da aka fafata a birnin Madrid har zuwa karshen sa.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu