Isa ga babban shafi

Nadal ya yi rashin nasara a Grand Slam karon farko cikin shekarar nan

Rafael Nadal ya sha kaye a karon farko a cikin shekarar nan ta 2022 karkashin babbar gasar Grand Slam ta bana, inda Frances Tiafoe ya doke shi a zagaye na hudu.

Dan wasan Tennis Rafel Nadal.
Dan wasan Tennis Rafel Nadal. © Pierre René-Worms
Talla

Ba’amurka Tiafoe ya bai wa magoya bayansa na gida mamaki a yayinda ya buge Nadal, wanda ya lashe gasar ta Grand Slam har sau 4 a tarihi, da ci 6-4 4-6 6-4 6-3 a karawar ta jiya da ta gudana a birnin New York.

Tiafoe zai kara da dan kasar Rasha, lamba 9 a duniya Andrey Rublev a wasan daf da kusa da karshe a garin Flushing Meadows na New York.

Tiafoe, wanda shi ne lamba na 22 a duniya ya yi wurgi da abin buga kwallonsa, ya rufe fuska cikin mamaki sakamakon nasarar da ya samu a kan wannan gwarzo da ya lashe manyan kofunan gasar tennis na Duniya har sau 22.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.