Tennis: An haramta wa 'yan wasan Rasha, Belarus fafatawa a Wimbledon
‘Yan wasan kwallon tennis daga Rasha da Belarus ba za su fafata a gasar Wimbledon ta wannan shekarar ba sakamakon mamayar Ukraine da Rasha ta yi.
Wallafawa ranar:
Lamba 2 na duniya a ajin maza, Daniil Medvedev na kasar Rasha da lamba 4 ta duniya a ajin mata, Aryna Sabalenka su ne manyan ‘yan wasan tennis da wannan lamari ya shafa.
Za a bari ‘yan wasa daga wadannan kasashe su fafata a gasar amma ba a karkashin tutar kasashen na su ba, a gasar Wimbledon da za a fara a ranar 27 ga watan Yuni zuwa 10 ga wata Yuli.
Nan gaba a wannan rana ta Laraba ce hukumar kula da wasan Tennis ta Ingila za ta tabbatar da wannan mataki.
Kakakin gwamnatin Rasha, Dmitry Peskov ya caccaki wannan matakin, yana mai cewa Rasha kasa ce mai karfi a harkar tennis, saboda haka maida ta saniyar ware zai rage armashin gasar.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu