Isa ga babban shafi
Wasanni-Tennis

Mai yiwuwa a dage gasar Tennis ta Wimbledon

Mai yiwuwa a dage ko kuma a soke gasar kwallon Tennis ta Wimbledon bayan da masu ruwa da tsaki suka shirya wani taron gaggawa da zai gudana a mako mai zuwa don tattauna yiwuwar yin gasar ta wannan shekarar a cikin wanan yanayi da cutar coronavirus ke yi wa duniya barazana.

Serena Williams ya Amurka, bayan ta lashe kofin Wmbledon Open sakamakon doke Victoria Azarenka a 2015.
Serena Williams ya Amurka, bayan ta lashe kofin Wmbledon Open sakamakon doke Victoria Azarenka a 2015. REUTERS/Toby Melville
Talla

A ranar 29 ga watan Yuni ne aka shirya za a fara wannan gasa, amma ci gaba da ta’azzarar wannan cuta ta coronavirus ta kawo cikas ga jadawalin wasanni da gasanni, kuma wannan gasa ta Wimbledon ka iya zama babbar gasa ta gaba da annobar za ta kawo wa jinkiri.

Gasar French Open ce ta farko cikin manyan gasannin Tennis na Grand Slam 3 da suka rage a wannan shekarar da aka dage sakamaakon wannan annobar.

Tun da farko, jadawalin gasar ta French Open wacce ake fafatawa a kan yumbu, ya nuna cewa daga ranar 24 ga watan Mayu zuwa 7 ga watan Yuni za a yi wannan gasa, amma hukumar kwallon Tennis ta Faransa ta dage ta zuwa 20 ga watan Satumba.

A gaba daya gasannin Tennis, gasar Wimbledon ce a ke wa kallon mafi girma, kuma alamu na nuni da cewa ba makawa za a jinkirta ta.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.