Isa ga babban shafi

Najeriya na shirin murmurowa daga shan kayenta a hannun Afrika ta kudu

Tawagar kwallon kafar Afrika ta kudu Banyana Banyana na shirin haduwa da Burundi yau alhamis bayan nasara kan Super Falcons ta Najeriya a litinin din da ta gabata a wani yanayi da ake ganin abu ne mai wuya Najeriyar ta sake sakacin rashin nasara.

Tawagar Super Falcons ta Najeriya.
Tawagar Super Falcons ta Najeriya. Pulse.ng
Talla

Ana saran tawagar ta Najeriya ta murmuro daga shan kayen na litinin yayin haduwarta da Bostwana a yau, duk da cewa za ta iya fuskantar tangarda saboda rashin zakarar tawagar wato Asisat Oshola da ta samu rauni a wasan na litinin.

Oshola mai shekaru 27 wadda ta lashe kyautar gwarzuwar Afrika sau 4, hukumar kwallon kafar Najeriya ta ce raunin ba zai bata damar taka leda a ilahirin wasannin gasar ba.

Duk da cewa itama Bostwanar ta yi rawar gani a haduwarta da Burundu inda suka tashi wasa 4 da 2, said ai ba lallai ta iya makamanciyar nasarar kan Super Falcons ba.

Tawagar ta Najeriya dai za ta so kawar da caccakar da ta ke ci gaba da fsukanta bayan rashin nasarar da kwallo 1 mai ban haushi, wanda ken una cewa za ta shiga wasan na yau da karfinta.

Wannan ne dai karon farko da Bostwana ke samun damar taka leda a gasar ta WAFCON.

Kocin Super Falcons Randy Waldrum ba’amurkiya ta ce tawagar za ta yi iyakar kokarinta don kaucewa shan kaye a karawar.

Idan har najeriya ta sake rashin nasara a karawar ta yau, akwai yiwuwar ta fice daga gasar tun a matakin rukuni.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.