Isa ga babban shafi

Afirka ta Kudu ta sha alwashin kawo karshen Najeriya a gasar WAFCON

Kocin tawagar kwallon kafar Afrika ta Kudu ta mata, Desiree Ellis, ta sha alwashin jagorantar ‘yan wasanta wajen lashe kofin gasar cin kodin kasashen Afirka ajin mata ta bana.

Kocin tawagar kwallon kafar Afrika ta Kudu ta mata, Desiree Ellis.
Kocin tawagar kwallon kafar Afrika ta Kudu ta mata, Desiree Ellis. © ANESH DEBIKY/AFP/Getty Images
Talla

A karshen makon nan aka tsara za a fara gasar ta WAFCON a kasar Morocco.

Sau biyar tawagar matan Afirka ta Kudun ke kammala gasar cin kofin Afirkan a matsayi na biyu, kuma uku daga cikin rashin nasarorin lashe gasar da suka yi, sun sha kaye ne a hannun takwarorinsu na Najeriya, Super Falcons.

Kuma a bana ma Afirka ta Kudun za ta sake karawa da Najeriya a rukuni na uku da suke tare da Burundi da kuma Bostwana.

Yayin wata ganawa da manema labarai, kocin ‘yan Afirka ta Kudun da aka fi sani da Banyana Banyana, t ace lokaci yayi da za su kawo karshen kaka-gidan da Najeriya ke yi a gasar ta WAFCON tsawon shekaru.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.