Zakarun Turai: Liverpool da Real Madrid za su yi karon batta a Paris
Yau za kece raini tsakanin Liverpool da Real Madrid a wasan karshe na gasar cin kofin zakarun Turai a birnin Paris.
Wallafawa ranar:
Liverpool dai na neman lashe kofin na gasar Zakarun Turai ne karo na 7, a yayin da Real Madrid ke fatan ta lashe kofin na 14.
Ana sa ran ‘yan kallo kimanin dubu 80 ne za su hallara a filin wasa na ‘Stade de France’ a birnin Paris domin ganin yadda za ta kaya a wannan babban wasa.
Jami'an 'yan sanda akalla dubu 7,000 ne za su kasance a bakin aiki domin tabbatar da doka da oda yayin fafatawar tsakanin Liverpool da Real Madrid.
Wasan, wanda shi ne irinsa karo na biyu da za a yi tsakanin tawagar ta Jurgen Klopp da Carlo Ancelotti, da fari an tsara buga shi ne a filin wasa na Gazprom da ke St Petersburg a Rasha, amma aka mayar da shi filin wasa na ‘Stade de France’ bayan da Rasha ta mamaye Ukraine a watan Fabrairu.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu