Isa ga babban shafi

Benzema ya ci kwallaye 41 cikin wasanni 41

Karim Benzema na ci gaba da kafa tarihi a Real Madrid, inda a wasan da suka fafata da Manchester City a ranar Laraba kadai ya kafa tarihin har kashi uku, domin kuwa adadin wasannin da ya bugawa kungiyarsa ya kai 600, daidai da tarihin da tsohon dan wasan Real Madrid Paco Gento ya kafa.

Karim Benzema.
Karim Benzema. © REUTERS/Jon Nazca
Talla

Zalika kwallaye biyun na Benzema ya jefa a ragar City ya sa jumilar wadanda ya ci a kakar wasa ta bana kaiwa kwallaye 41 a cikin wasanni 41 da ya buga a bana.

Da wadannan kwallaye 41, Benzema ya zama dan wasa na biyar da ya kai wannan adadi cikin kakar wasa guda a tarihin Real Madrid, bayan Cristiano Ronaldo, Ferenc Puskas, Alfredo Di Stefano da Hugo Sanchez.

Benzema na kuma gaf da zarce Raul Gonzales a matsayin dan Real Madrid na biyu da ya fi ci wa kungiyar kwallaye, bayan Cristiano Ronaldo, inda a yanzu dan wasan ke da adadin kwallaye 320, yayin da Raul ya ci wa Madrid kwallaye 323.

Sai dai kuma a iya cewa bajintar tauraron na Real Madrid ta fi armashi a gasar zakarun Turai wadda ake ganin ta bana ce mafi kayartarwa gareshi, domin kuwa a yanzu haka yana da kwallaye 14 a gasar, abinda ya sa shi zama mafi yawan kwallaye a bana, yayin da Robert Lewondoski na Bayern Munich ke biye da kwallaye 12.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.