Isa ga babban shafi
Wasanni

Benzema ya kori PSG daga gasar Zakarun Turai

Tauraron Real Madrid kuma dan wasan gaba na kungiyar Karim Benzema, ya zura kwallaye uku rigis a ragar Paris Saint Germain, kwallayen da suka yi sanadin ficewar kungiyar ta Faransa daga gasar cin kofin zakarun Turai ta bana.

Karim Benzema, yayin murnar nasarar jefa kwallaye a ragar PSG.
Karim Benzema, yayin murnar nasarar jefa kwallaye a ragar PSG. REUTERS - SUSANA VERA
Talla

Real Madrid ta samu nasarar lallasa PSG ne da kuma kaiwa zuwa zagayen kwata final ne bayan rama kwallaye biyun da bakin na Faransa suka fara jefa musu a daren ranar Laraba a filin was ana Santiago Bernabeu.

A zagayen farko na karawar da suka yi a Faransa dai, PSG ce ta doke Madrid da kwallo 1-0, yayin da kuma a karawa da biyu Zakarun na La Liga suka lallasa PSG da kwallaye 3-1.

Karim Benzema, a yayin jefa kwallon farko a ragar kungiyar Paris Saint-Germain, a zagaye na biyu na gasar zakarun Turai.
Karim Benzema, a yayin jefa kwallon farko a ragar kungiyar Paris Saint-Germain, a zagaye na biyu na gasar zakarun Turai. REUTERS - SUSANA VERA

Bayan kimanin sa’a 1 da fara karawar da suka yi a daren ranar Laraba, mai tsaron ragar PSG Gianluigi Donnarumma yayi kuskuren da ya baiwa Benzama damar jefa kwallon farko.

Dan wasan gaban na tawagar kwallon kafar Faransa ya kara kwallo ta biyu da ta uku ne kuma a cikin mintuna biyu kacal, abinda ya sa aka tashi wasan Real Madrid na da jumillar kwallaye 3, PSG kuma 2.

Kwallaye ukun da Benzema ya jefawa PSG ya sanya adadin wadanda ya ci wa kungiyar tasa a jumlace kaiwa 309, inda ya wuce Alfredo Di Stefano da ya ci 308.

Kwallo ta farko da Benzema ya ci wa Real Madrid ita ce wadda ya jefa a ragar kungiyar Xeres da ke La Liga a ranar 20 ga Satumban shekarar 2009, kuma Ruud van Nistelrooy ne ya taimaka wa dan wasan a waccan lokaci.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.