Isa ga babban shafi

Real Madrid za ta iya lashe kofin gasar zakarun Turai - Ancelotti

Kocin Real Madrid Carlo Ancelotti ya bayyana cewar babu shakkah karawar da za su yi karo na biyu da Chelsea a wannan Talata, wasa ne da ba zai yi sauki ba, sai dai ya bayyana kwarin gwiwar kungiyar ta sa za ta iya lashe kofin gasar Zakarun Turai ta bana.

Kocin Real Madrid Carlo Ancelotti.
Kocin Real Madrid Carlo Ancelotti. AFP
Talla

A zagayen farko na fafatawar da suka yi, Madrid ce ta samu nasara kan Chelsea da kwallaye 3-1.

Shi da kansa kocin kungiyar ta Chelsea Thomas Tuchel ya yarda cewa akwai jan aiki a gabansu kafin nasarar kaiwa zagayen semi Final na gasar zakarun Turai.

Tarihi ya nun cewar babu wata kungiya ta Ingila da ta taba cin kwallo fiye da daya a filin wasa na Santiago Bernabeu ba, a gasar cin kofin zakarun Turai, wanda hakan ya sa wasu masu sharhi kan kwallon kafa ke ganin Real Madrid ke kan gaba wajen zuwa wasan kusa da na karshe.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.