Isa ga babban shafi

Villarreal ta doke Bayern Munich da 1-0 a gasar zakarun Turai

Villarreal ta lallasa Bayern Munich da ci 1-0 yayin fafatwarsu cikin zagaye na farko na wasan kwata Final a gasar neman cin kofin zakarun Turai a jiya Laraba.

Dan wasan Bayern Munich Thomas Muller bayan rasa damar jefa kwallo a ragar kungiyar Villareal
Dan wasan Bayern Munich Thomas Muller bayan rasa damar jefa kwallo a ragar kungiyar Villareal © Photo by Chris Brunskill/Fantasista/Getty Images
Talla

Arnaut Danjuma ne ya zura kwallon daya a ragar Bayern a minti na 8 da fara karawar ta su, yayin wasan da ya ba da mamaki.

Sai a mako mai zuwa ne wato 12 ga watan Afrilu Bayern Munich za ta karbi bakuncin Villareal a Jamus domin sake karawa a karo na biyu.

Har yanzu dai wasu na kallon Munich masu kofin Zakarun Turai guda shida a matsayin wadanda za su yi nasarar tsallakawa zuwa zagayen wasan kusa da na karshe, bayan karawar da za su sake yi da Villareal a filin wasa na Allianz Arena.

A baya dai ana kallon tawagar kungiyar ta Spain dake karkashin Unai Emery a matsayin daya daga cikin mafi saukin abokan hamayyar da aka samu a yayin da ake gamin gambizar zabar kungiyoyin da za su kara da juna a zagayen kwata final na gasar Zakarun Turai, inda za a iya cewa watakila Benfica ce kawai ke kasa da su.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.