Isa ga babban shafi
Gasar Zakarun Turai

Za mu dauki fansar abin da Madrid ta yi mana a 2018 - Salah

Dan wasan gaba na Liverpool, Mohamed Salah na shirya kansa don yin ramuwar gayya kan Real Madrid yayin wasan karshe na gasar zakarun Turai na wannan watan.

Dan wasan gaba na Masar da Liveerpool Mohamed Salah.
Dan wasan gaba na Masar da Liveerpool Mohamed Salah. REUTERS - AMR ABDALLAH DALSH
Talla

Mohammed Salah, wanda ya karbi kyautar gwarzon dan wasan kwallon kafa na shekara a Landan ranar Alhamis, ya fice daga fili yayin wasan karshe da Madrid ta doke su a shekarar 2018 a Kyiv bayan rauni da Sergio Ramos yayi masa.

Yanzu dai kungiyoyin biyu, wadanda suka raba kambun gasar 19 a tsakaninsu, za su kara ne a wasan karshe na bana a birnin Paris a ranar 28 ga watan Mayu bayan da Real ta yi nasara a kan Manchester City a ranar Laraba da kuma nasara da Liverpool ta yi a kan Villarreal.

'Yan wasan Real Madrid yayin murnar samun nasarar kaiwa wasan karshe na gasar Zakarun Turai bayan doke Manchester City da jumillar kwallaye 6-5.
'Yan wasan Real Madrid yayin murnar samun nasarar kaiwa wasan karshe na gasar Zakarun Turai bayan doke Manchester City da jumillar kwallaye 6-5. © REUTERS/Isabel Infantes

Dan wasan na Masar Salah, mai shekara 29, da aka tambaye shi ko yana ganin wasan karshe a matsayin wata dama ce da Liverpool za ta iya daukar fansa a kan kashin da ta sha a shekaru hudu da suka wuce daga Madrid, ya ce, “Eh, lallai wannan wata damace na daukar Fansa .

"Na yi farin ciki sosai, na fada kafin wasan cewa ina so in kara da Madrid a wasan karshe".

"Na tabbata wasan zai kasance mai tsauri, saboda sun doke kungiyoyi masu kyau don haka zamu mai da hankali sosai "

Liverpool na neman lashe kofuna hudu da ba a taba ganin irinsa ba na dukkan manyan kofunan Ingila hudu a kakar wasa daya.

A halin yanzu kungiyar Jurgen Klopp tazarar maki daya ne kawai tsakanin sa da Manchester City jagorar gasar Premier, kuma za su kara da Chelsea a wasan karshe na cin kofin FA, bayan da suka lashe kofin League.

Dan wasan gaba na Manchester City Raheem Sterling (tsakiyar) zai fafata da 'yan wasan Chelsea N'Golo Kanté (hagu) da Cesar Azpilicueta (dama) a ranar 8 ga Mayu, 2021.
Dan wasan gaba na Manchester City Raheem Sterling (tsakiyar) zai fafata da 'yan wasan Chelsea N'Golo Kanté (hagu) da Cesar Azpilicueta (dama) a ranar 8 ga Mayu, 2021. AP - Shaun Botterill

Wannan shi ne karo na biyu da Salah ya lashe kyautar FWA ta maza, wanda aka fara tun shekarar 1948, bayan ya karbi ta farko shekaru hudu da suka wuce.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.