Isa ga babban shafi
City - Madrid

Zakarun Turai: Za'a rubuta sabon tarihi tsakanin Madrid da City

Manchester City za ta karbi bakuncin Real Madrid a filin wasa na Etihad a yammacin wannan Talata a zagen farko na wasan kusa dana karshe na gasar cin kofin zakarun Turai. Zakarun gasar Premier sun casa Atletico Madrid a wasan daf da na kusa da na karshe a gasar, yayin da Real Madrid ta doke Chelsea kafin zuwa wannan matsayi na Semi-Final.

Tambarin gasar cin kofin Zakarun Turai ta Champions League dake gudana a karkashin hukumar UEFA.
Tambarin gasar cin kofin Zakarun Turai ta Champions League dake gudana a karkashin hukumar UEFA. AP - Claude Paris
Talla

Man City za ta yi kokarin amfani da damar samun nasara a wasan farko a gidanta kafin wasan da za a yi a gidan Madrid a ranar 4 ga watan Mayu, don zuwa wasan karshe da kungiyoyin ingila biyu ko kuma na Spain biyu zasu hadu a bana, yayin da Liverpool da Villarreal ke shirin fafatawa a wannan Laraba.

Kocin Manchester City Pep Guardiola ya tattauna da Phil Foden na Manchester City yayin wasan ƙwallon ƙafa na zagaye na biyu na gasar zakarun Turai tsakanin Atletico Madrid da Manchester City a filin wasa na Wanda Metropolitano da ke Madrid, Spain, Laraba, 13 ga Afrilu, 2022. (AP Photo/Manu Fernandez)
Kocin Manchester City Pep Guardiola ya tattauna da Phil Foden na Manchester City yayin wasan ƙwallon ƙafa na zagaye na biyu na gasar zakarun Turai tsakanin Atletico Madrid da Manchester City a filin wasa na Wanda Metropolitano da ke Madrid, Spain, Laraba, 13 ga Afrilu, 2022. (AP Photo/Manu Fernandez) AP - Manu Fernandez

Tarihin haduwar kungiyoyin biyu

Sau shida Manchester City da Real Madrid suka hadu a baya, kuma kowa ya yi nasara sau biyu, yayin da sukayi canjaras sau biyu.

Haduwar Farko

Ganawarsu ta farko ta zo ne a matakin rukuni na gasar cin kofin zakarun Turai na shekarar 2012-13, inda Real Madrid ta ci 3-2 a Bernabeu kafin a raba maki a karawar da suka yi a Manchester watanni biyu bayan haka.

Dan wasan gaba na Real Madrid Karim Benzema.
Dan wasan gaba na Real Madrid Karim Benzema. REUTERS - JUAN MEDINA

Haduwar ta biyu

Ƙungiyoyin biyu sun sake haduwa a wasan kusa da na karshe na gasar Champion League a 2015-16; karawar ta farko dai ta kare ne babu ci a filin wasa na Etihad kafin Los Blancos ta yi nasara a wasa na biyu da ci 1-0 a Bernabeu sakamakon kwallon da Fernando ya ci gida.

Haduwar karshe

Bangarorin biyu sunyi haduwar karshe a matakin zagaye na ‘yan 16 na gasar zakarun Turai a shekarar 2019-20; Man City ta yi nasara a karawar farko da ci 2-1 a Madrid ta kuma kara ci a gida da ci 2-1 a watan Agustan 2020, wanda ya bata jimillar kwallaye  4-2.

Madrid bata taba cin City a Etihad ba

Real Madrid bata taba nasara kan city a Etihad ba, wato filin wasanta na gida, inda ta ci daya kuma ta yi canjaras a wasanni biyun ukun da suka kara.

Gabaɗaya:

Man City - nasara sau biyu

Real Madrid - nasara sau biyu 

Canjaras - sau biyu

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.