Isa ga babban shafi
Kwallon Kafa-Gasar Zakarun Turai

Zakarun Turai: Manchester City ta yi wa Atletico Madrid 1 mai ban haushi

Kwallon da Kevin de Bruyne ya ci bayan hutun rabin lokaci ya bai wa Manchester City nasara a kan Atletico Madrid a wasan daf da na kusa da karshe na gasar cin kofin zakarun nahiyar Turai, haduwa ta farko a filin wasa na Etihad a daren Talata.

Kevin de Bruyne,dan wasan Manchester City da ya jefa kwallo a ragar Benfica a daren Talata.
Kevin de Bruyne,dan wasan Manchester City da ya jefa kwallo a ragar Benfica a daren Talata. © Dave Thompson/AP
Talla

‘Yan wasan Atletico, karkashin jagorancin mai horaswa Diego Simeone sun yi irin  salon wasan da aka san su da shi, wato salon tsaron baya, inda suka turje wa City, suka takaita damamakinsu har sai da wankin hula ya nemi ya kai su dare, kafin daga bisani de Bruyne ya saka kwallo a ragarsu ana saura mintuna 20 a tashi wasan.

Sanya Phil Foden da mai horaswa Pep Guardiola ya yi ne ya bai wa City damar saka kwallo daya tilo ta wasan, domin kuwa shi ne ya gara wa de Bryune kwallon da ya zura wa mai tsaron ragar Atletico, Jan Oblak.

Lokaci ne mai armashi a wasan, musamman ma ganin irin yadda mai horar da City, Guardiola ya yi murnar jefa kwallon, wanda ke nuni da yadda suke matukar neman nasara a wasan, ko da kuwa ‘yar kankanuwa ce, ganin cewa akwai jan aiki a gabansu idan suka ziyarci filin wasa na Wanda Metropolitano na birninn Madrid na Spain a haduwa ta 2.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.