Madrid ta haye wasan daf da na karshe a gasar zakarun Turai
Real Madrid ta kawo karshen Chelsea mai rike da kambin gasar zakarun Turai, duk da da ta yi a kanta da 3-2 a daren jiya a Santiago Bernabeu, ta kuma haye wasan semi-final.
Wallafawa ranar:
Chelsea taga ta leko ta koma a jiyan duk da kwallaye uku da ta taci ta hannun Mason Mount da Antonio Rudiger da kuma Timo Werner.
Kwallo da Karim Benzema ya zura a karin lokaci ya fitarwa Real Madrid kitse a wuta, bayan wanda Rodrygo ya zura a mintuna ta 80.
Yanzu haka Dan wasan na Faransa Karim Benzema ya zura kwallo hudu kenan a ragar Chelsea a haduwa biyun da suka yi na wasan daf da na kusa na karshe.
A wasan farko da suka buga ranar 6 ga watan Afirilu, Real Madrid ce ta yi nasara da ci 3-1 a fafatawar da suka yi a Stamford Bridge.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu