Isa ga babban shafi

Dole mu shiryawa karawa ta biyu da Manchester City - Ancelotti

Kocin Real Madrid Carlo Ancelotti ya ce ya zama dole su shiryawa haduwarsu ta biyu da Manchester City a Spain, inda suke fatan maimaita abin mamakin da suka yi a wasannin da suka kara da kungiyoyin PSG da kuma Chelsea a kokarinsu na kaiwa zagayen karshe na gasar cin kofin zakarun Turai.

Mai horas da Real Madrid Carlo Ancelotti.
Mai horas da Real Madrid Carlo Ancelotti. Reuters/Michaela Rehle
Talla

Ancelotti yayi wannan tsokaci ne yayin zantawa da manema labarai, bayan wasan zagayen kusa da na karshe a daren jiya Talata da Manchester City ta samu nasara kan Real Madrid da kwallaye 4-3 a filin was ana Etihad.

Masu masharhanta wasanni dai na ganin Madrid ta yi sa’a la’akari da cewar City mai masaukin baki ta rasa damarmaki da dama da ya kamata a ce ta jefa kwallaye da dama, abinda ya karawa jagororin na gasar La Liga karfin gwiwar cewa za su iya sauya sakamakon idan suka sake haduwa a Spain.

Tarihi dai ya nuna cewar Real Madrid ba ta taba samun nasarar doke Manchester City a filin wasa na Etihad da ke Ingila ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.