Liverpool na gab da kaiwa wasan karshe na gasar zakarun Turai
Liverpool na gab da zuwa wasan karshe na gasar cin kofin zakarun Turai karo na uku a cikin shekaru biyar, bayan da ta samu nasara kan Villarreal da 2-0, a wasan farko na zagayen kusa da na karshe da suka fafata a filin wasa na Anfield a ranar Laraba.
Wallafawa ranar:
Liverpool ta ci kwallayen biyu ne cikin mintuna biyu, ta hannun ‘yan wasanta Jordan Henderson da Sadio Mane.
A yanzu haka dai a iya cewar kungiyar ta Liverpool na da damar lashe jumillar kofuna har guda hudu a kakar wasa ta bana, domin kuwa bayan fatan kaiwa wasan karshe na gasar zakarun Turai, tazarar maki 1 kacal Manchester City ta baiwa Liverpool din a gasar Firimiyar Ingila wadda ya rage wasanni 4 a kammala ta.
Tuni dai Liverpool din ta lashe kofin Carabao. Akwai kuma gasar cin kofin kofin FA, da za ta fafata wasan karshenta ta Chelsea a ranar 14 ga watan Mayu.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu