Isa ga babban shafi
Zakarun Turai

Liverpool sun lallasa Benfica a matakin daf da kusa da karshe

Liverpool sun doke Benfica 1-3 har gida a wasan daf da na kusa da karshe na gasar zakarun Turai, haduwa na 2 da suka gwabza a birnin Lisbon na kasar Portugal a daren Talata.

Dan wasan Liverpool da Senegal  Sadio Mané a lokacin da ya doshi ragar Benfica a wasan daf da kusa da karshe na gasar Zakaru Turaia birnin Lisbon. 2022-04-06.
Dan wasan Liverpool da Senegal Sadio Mané a lokacin da ya doshi ragar Benfica a wasan daf da kusa da karshe na gasar Zakaru Turaia birnin Lisbon. 2022-04-06. Action Images via Reuters - MATTHEW CHILDS
Talla

Kwallon da Luis Diaz ya ci a kusan karshen wasan ta jaddada nasarar da Liverpool suka samu, kuma duk da haka mai tsaron ragar Benfica Odysseas Vlachodimos ne ma ya hana kwallayen Liverpool su fi haka sakamakon yadda ya yi ta ture kwallaye waje.

Ibrahima Konate ya yi tsalle sosai, inda ya saka wata kwallo kai zuwa ragar masu masaukin bakin, bayan nan kuma Sadio Mane ya kara wata kwallo duk kafin hutu, lamarin da ya sanyaya gwiwowin magoya bayan Benfica da suka cika filin wasa na Estadio da Luz.

Sai dai magoya bayan sun lalubo sabon karsashi biyo bayan kuskuren da Konate ya yi, wanda ya bai wa Drawin Nunez damar saka kwallo daya a ragar Liverpool.

Amma Liverpool za su kasance a sama a yayin da za su karbi bakuncin Benfica a haduwa ta 2 a filin wasa na Anfield da ke birnin Liverpool a Laraba mai zuwa, sai dai kocin Liverpool din Jurgen Klopp na cewa za su ci gaba da dagiya don gudun kada su sha mamaki a gidansu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.