Isa ga babban shafi
Wasanni-Kwallon Kafa

Liverpool ta tsallaka rukunin kungiyoyi 8 duk da rashin nasara kan Inter Milan

Duk da rashin nasarar Liverpool hannun Inter Milan da kwallo 1 mai ban haushi har Anfield hakan bai hana tawagar Jurgen Klopp tsallakawa matakin gab da na kusa da karshe na gasar cin kofin zakarun Turai ba.

Wannan ne karon farko cikin shekara guda da Liverpool ta yi rashin nasara a Anfield.
Wannan ne karon farko cikin shekara guda da Liverpool ta yi rashin nasara a Anfield. REUTERS - ALESSANDRO GAROFALO
Talla

A haduwar farko dai Liverpool ke jagoranci da kwallaye 2 da nema wanda ‘yan wasanta Roberto Firmino da Mohamed Salah suka zura mata cikin watan jiya a gidan Milan, lamarin da ke nuna a jumulla kungiyoyin biyu sun karkare wasan da kwallo 2 da 1.

Lautaro Martinez ya zurawa Milan kwallonta guda bayan dawowa daga hutun rabin lokaci duk da cewa tawagar tasa ta gama wasan na jiya da mutum 10 saboda yadda aka baiwa Alexis Sanches katunan gargadi har sau biyu.

Yayin wasan na jiya wanda Thiago Alcantara da Joel Matip suka shiga bayan murmurewa daga jiyar rauni, Liverpool ta yi kokarin zura kwallo tun gabanin tafiya hutun rabin lokaci ta hannun dan wasanta Mohamed Salah amma kuma kwallon ta bugi karfen raga, haka zalika Diogo Jota ya so farkewa bayan dawowa daga hutun rabin lokaci.

To shi ma dai tauraron Liverpool Mohammed Salah ya ce ko shakka babu shan kayen nasu hannun Inter Milan zai kara musu kaimi wajen ganin sun gyara kura-kuransu a wasan da ke tunkarosu nan gaba.

Kofin na zakarun Turai na jerin kofunan da Liverpool ke fatar dagewa a wannan kaka kari kan Firimiya da FA, wadanda dukkaninsu ta ke ci gaba da nuna bajinta.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.