Isa ga babban shafi

Okagbare ta gaza daukaka kara kan haramta mata wasannin shekaru 10

Fitacciyar 'yar wasan tseren Najeriya Blessing Okagbare, ta gaza daukaka kara kan hukuncin haramcin shiga wasanni na tsawon shekaru 10 da kotun ladabtarwa a harkar wasannin guje-guje da tsalle-tsalle AIU ta yanke mata.

Blessing Okagbare fitacciyar 'yar tseren gudu da wasu fannonin wasannin motsa jiki da ke wakiltar Najeriya.
Blessing Okagbare fitacciyar 'yar tseren gudu da wasu fannonin wasannin motsa jiki da ke wakiltar Najeriya. REUTERS/Paul Hackett
Talla

Okagbare ‘yar shekaru 33, ta gamu da hukuncin ne bayan da gwajin likitoci ya tabbatar da cewar tana shan haramtattun kwayoyin karin kuzari domin samun nasara a wasu daga cikin wasannin da ta rika fafatawa, abinda ya sa aka lafta mata haramcin shiga wasannin motsa jikin na tsawon shekaru biyar.

Haramcin karin shekaru biyar ya hau kan 'yar tseren ne kuma, bayan samun ta da laifin kin ba da hadin kai ga binciken da ake yi kan zarge zargen da ake mata.

A baya dai Okagbare ta yi barazanar daukaka kara kan hukuncin zuwa gaban kotun sauraron kararrakin wasanni a cikin kwanaki 30, wa’adin da ya wuce ranar 18 ga Maris da muke ba tare da 'yar tseren ta dauki matakin ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.