Isa ga babban shafi
Tseren gudu

Okagbare na gaf da rasa damar daukaka kara kan haramta mata wasanni

Mai yiwuwa fitacciyar 'yar tseren gudu ta Najeriya, Blessing Okagbare, ba za ta daukaka kara kan hukuncin dakatar da ita daga wasanni na tsawon shekaru 10 da hukumar kula da tantance nagartar ‘yan wasan motsa jiki AIU ta yi mata ba, kan amfani da haramtattun kwayoyi masu kara kuzari.

Blessing Okagbare fitacciyar mai tseren gudu 'yar Najeriya.
Blessing Okagbare fitacciyar mai tseren gudu 'yar Najeriya. REUTERS/Andrew Winning
Talla

A ranar 18 ga Fabrairu aka dakatar da Okagbare saboda saba dokokin hana shan kwayoyin kara kuzari abinda ya sanya aka dakatar da ita daga shiga wasanni tsawon shekaru biyar bayan gwajin da aka yi mata a ranar 19 ga Yuli, na shekarar 2020.

Haramcin karin shekaru biyar na wasanni kuma ya hau kan ‘yar tseren Najeriyar ne saboda samunta da laifin kin ba da hadin kai ga masu bincike.

Cikin wani sako da ta wallafa a shafukanta na sada zumunta Okagbare ta ce lauyoyinta na nazarin matakin da za su dauka a nan gaba.

A halin yanzu dai wa’adin kwanaki 30 da suka ragewa ‘yar Najeriyar domin daukaka kara na gaf da cika.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.