Isa ga babban shafi
Wasanni - Najeriya

An haramtawa 'yar Najeriya shiga wasannin motsa jiki tsawon shekaru 10

Hukumar yaki da shan haramtattun kwayoyin karin kuzari a wasannin motsa jiki ta duniya wato AIU, ta haramtawa fitacciyar ‘yar wasan motsa jiki ta Najeriya, Blessing Okagbare shiga wasanni har tsawon shekaru 10, bisa samunta da ha’inci wajen shan haramtattun kwayoyin.

Blessing Okagbare, fitacciyar ‘yar wasan motsa jiki ta Najeriya.
Blessing Okagbare, fitacciyar ‘yar wasan motsa jiki ta Najeriya. © REUTERS/Aleksandra Szmigiel
Talla

Okagbare 'yar shekaru 33, wadda ta kuma yi fice a fannin tseren gudu, an kore ta daga gasar Olympics da ta gudana a birnin Tokyo cikin shekarar 2021 kafin zagayen kusa da na karshe na tseren mita 100 ajin mata, bayan da sakamakon wani gwaji da aa yi mata cikin watan Yuli a Slovakia ya gano ta sha kwayar kara kuzarin sinadaran jikin dan Adam.

‘Yar Najeriyar dai ta taba lashe lambar Azurfa a gasar Olympics ta shekarar 2008.

Okagbare ta tsinci kanta cikin halin tsaka mai wuya ne duk da cewar ba a bayyana sunanta cikin wata tuhuma da aka gabatar ba a Amurka cikin watan da ya gabata a kan wani likita mazaunin birnin Texas, Eric Lira, da ke samarwa ‘yar Najeriyar kwayoyin.

Jami'an ma'aikatar shari'ar Amurka a New York sun ce Eric Lira, mai shekaru 41 wanda ke zaune a El Paso, ya baiwa 'yan wasa biyu magunguna karin kuzari da zummar taimaka musu wajen tafka magudi a yayin wasannin motsa jikin gasar Olympiics a Tokyo.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.